Bankin Duniya ya yi gargadin cewa Najeriya na iya fuskantar barazanar rayuwa.
Bankin na kasa da kasa ya yi gargadin cewa idan Najeriya ta gaza inganta tsarin harajin ta da kuma mai da hankali kan wasu fannoni don bunkasa kudaden shiga, za'a samu cigaba da durkushewar kudaden shiga wanda dama ake da karancin gaske.
Bayanai sunyi uni da cewa, duk da hauhawar farashin man fetur a kasuwannin duniya, Najeriya ba ta ci gajiyar haka ba saboda makudan kudaden da ake kashewa wajen tallafin man fetur.
Wani kwararren Jami'i a bankin duniya, Mista Rajul Awasthi, ya bayyana hakan a wani taro na kasa da kasa wanda kungiyar Tattalin Arzikin Najeriya ta shirya a ranar Laraba.
Ya ce dole ne Najeriya ta kawar da tsarin tallafin mai.
(Karin Magana: Da sassafe ake kama fara)