Tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi na biyu, ya ce Najeriya ta rasa samun damammaki da dama saboda rashin zaben mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a matsayin shugaban taraiyyar kasar nan.
Tsohon sarkin ya baiyana haka ne a yayin kaddamar da wani littafi wanda aka wallafa kan mataimakin shugaban kasar a jiya.
A cewarsa, Gazawar tsarin siyasa wajen marawa Osinbajo baya a matsayin shugaban kasa ya sa Najeriya ta kara samun kanta cikin yanayi na tabarbarewa.
Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya,Ya baiyana cewar yana day akin cewa Osinbajo na daya daga cikin wadanda ke cikin gwamnati mai ci, da ke da ra'ayin yin muhawara a kan ko wane irin lamari da kuma bayar da hujja mai inganci kan yadda za’a samu cigaban kasa.