Najeriya ta gaza cimma burinta na samun karin guraben kujerun aikin hajjin bana daga hukumomin Kasar Saudiyya.
A ci gaba da kokarin cika alkawarin da hukumar aikin Hajji ta kasa NAHCON ta yi na samo karin kujerun aikin Hajin bana daga kasar Saudiyya, kwamishinan hukumar ta NAHCON, Alhaji Abdullahi Magaji Hardawa ya jagoranci wata tawaga domin gabatar da bukatar ga hukumomin Saudiyya.
Ziyarar ta zama mai mahimmanci musamman domin magance korafe-koren da ga kamfanoni matafiya kan Karancin kujerun aikin Hajjin a bana.
Sai dai a cikin wata sanarwa da Mataimakiyar daraktar sadarwa da hulda da jama'a Fatima Sanda ta fitar, tace bayan ganawa da wakilan hukumar NAHCON sukayi da Ministan Hajji da Umrah na Saudiyya, alkawarin bai tabbata ba.
Saboda haka, Maniyata daga Nijeriya dubu 43 da 8 zasu shiga Kasar Saudiyya domin sauke faralli a bana.
Dangane da haka NAHCON ta bukaci al'umma da abin ya shafa su fahimci halin da ake ciki inda NAHCON ta roki da su karbi hakan amatsayin nufin Ubangiji sannan a jira Lokaci na gaba.
Hukumar tace ta iya kokarinta amma kaddara ta riga fata.
Haka kuma sanarwar tace shugaban hukumar NAHCON Alhaji Zikrullah Kunle Hassan da sauran jami’an hukumar sun yi iya kokarinsu wajen ganin an raba kujerun cikin adalci. sai dai tun farko a fili yake cewa ba duk wanda ya cancanta ne zai je aikin Hajjin bana ba saboda karancin guraben da aka ware.