On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Najeriya Ta Fuskanci Asarar Trilliyan 1.3 Cikin Watan Agusta Kadai Saboda Ayyukan Barayi Da Masu Fasa Bututun Man Fetur - Majalissa

Najeriya ta yi asarar Naira Tiriliyan 1.3 sanadiyar satar man fetur tsakanin watan Janairu zuwa Agusta na wannan shekara kadai.

Wannan dai ya fito ne a wani rahoto na kwamitin wucin gadi da Majalisar Dattawa ta kafa domin gudanar da cikakken bincike kan satar mai a kasarnan.

Sanata Albert Bassey Akpan, wanda shi ne shugaban kwamitin, ya shaida wa manema labarai a ranar Talata cewa, satar man fetur ya durkusar da yadda ake hako mai a kasarnan kuma ya yi sanadin asarar kusan dala biliyan 2 a bana kadai.

‘Dan majalisar ya ce an rufe manyan wuraren fitar da kayayyaki sama da watanni bakwai saboda fasa bututun mai da kuma satar mai.

Sai dai ya ce babu laifi idan aka hada kai da wasu bangarori da ba na gwamnati ba wajen tabbatar da bututun mai domin za’a  samu sakamako mai kyau.