Kawo yanzu gwamnatin taraiyya ta baiyana cewar ta kashe zunzurutun kudi har Dala Milyan 1 da Dubu 200 domin yin hayar motocin Safa wadanda zasu kwaso ‘yan Najeriyar da suka makale daga kasar Sudan mai fama da yaki zuwa iyakon kasar Masar , wanda kuma daga nan ne za’a dauko su ta cikin jirgi zuwa gida Najeriya.
Babban sakatare a ma’aikatar kula da harkokin Jin kai da kare afkuwar Bala’oi ta kasa, Nasir Sani Gwarzo ne ya baiyana haka, jim kadan bayan kammala wata ganawar sirri a ma’aikatar dake Abuja.
Ya ce daga cikin motocin Safa 40 da aka yi amfani da su domin kwaso ‘Yan Najeriyar da suka makale a Sudan, An biya kowace Mota daya Dala Dubu 30.
Ya kara da cewar tsaikon da ‘yan Najeriyar suka fuskanta akan iyakokin kasar Masar ya biyo bayan cika sharuddan babban bankin kasa, Yana mai cewar babu yadda za’a yi a tura kudi kai tsaye zuwa kasar Sudan,Dole ne sai anyi amfani da Dan kai sako.