Gwamnatin tarayya ta amince da sabuwar allurar rigakafin zazzabin cizon sauro daga jami’ar Oxford, inda ta zama kasa ta biyu a duniya da ta amince da hakan.
Alurar rigakafin-R21/Matrix-M, Jami'ar Oxford ce ta samar da ita kuma Cibiyar Serum ta Indiya ta kera.
Darakta Janar ta Hukumar Kula da Abinci da Magunguna a kasarnan NAFDAC, Mojisola Adeyeye, itace ta sanar da ci gaban ranar Litinin a Abuja.
Mojisola Adeyeye ta ce an yi allurar rigakafin cutar zazzabin cizon sauron zata kasance ga yara daga watanni 5 zuwa watanni 36.
Adeyeye ta ce, NAFDAC ta karbi samfurin R21 kuma zata yi nazari mai zaman kansa daga kwararru daga manyan makarantun Najeriya da kuma kwamitin binciken alluran rigakafi na cikin gida na hukumar.