Gwamnatin taraiyya ta ce balaguron da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi zuwa kasashen waje, ta kawo ma kasar nan cigaba da dama, ta bangaren cigaban tattalin arzikin kasa.
Ministan Kasashen Waje , Geoffrey Onyema ne ya baiyana haka yau a Abuja a lokacin da yake gabatar da irin nasarorin da ma’aikatarsa ta samu, a karkashin gwamnati mai ci.
Onyema ya ce balaguron da shugaban kasar yay i zuwa kasashen waje, inda ya gana da shugabannin kasashen bata tsaya ga iya jawo hankalin masu zuba jari zuwa kasar nan kadai ba, harma da daga martabar da Najeriya ke dashi.
Ya kara da cewa, gwamnatin taraiyya ta karkashin ma’aikatarsa ta samar da shirye-shirye da dama wadanda suka temaka wajen kare rayuwar ‘yan Najeriya dake zaune a kasashen waje.