On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Najeriya Na Gab Da Samun Lamunin Dala Bilyan 1 Da Rabi Daga Bankin Duniya

Gwamnatin tarayya na gab da samun tallafin dala biliyan 1 da rabi daga bankin duniya domin aiwatar da kasafin Kudi.

Ministan Kudi da kuma Tattalin Arziki, Wale Edun ne ya tabbatar da haka  a gefen taron shekara shekara na asusun bada lamuni na duniya (IMF) hadin gwiwa  da bankin duniya da aka gudanar a kasar Morocco, a jiya.

Ya ce lamunin na kasashe matalauta ne, da ba  za a saka masu  kudin ruwa wajen biyan bashin ba, Wanda kuma Najeriya ta cancanci shiga cikin jerin kasashen da za su iya samun rancen kudaden da bankin duniya ya saba  bayarwa.

Ministan ya kuma kara da cewar za'a tattauna sauran tsare-tsare na samar da kudade a yayin taron Majalisar Zartarwa na kasa da za'a gabatar a yau Litinin.