
Biyo bayan sace wasu manoma 20 da aka yi a Abuja ranar Alhamis, kungiyar manoma ta Kasa, AFAN, Ta yi gargadin cewa zai yi wahala ‘yan Najeriya su iya ciyar da kansu idan ba a yi wani abu da zai kare manoma a fadin kasar nan ba.
Da yake zantawa da manema labarai a jiya, Shugaban kungiyar AFAN na kasa, Arc Kabir Ibrahim, ya ce halin da manoma ke ciki, musamman a yankunan karkara ya dauki wani yanayi mai ban tsoro wanda ya zama wajibi a dauki matakan da suka dace.
Ibrahim ya kara da cewa Da Yuyuwar abincin da za’a samar a bana yayi karanci wanda hakan zai haifar ga yunwa da karin laifuka idan ba a yi wani abu cikin gaggawa domin samar da mafita a matakin Kananan Hukumomi da jihohi da kuma Taraiyya.