Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce Najeriya za ta bukaci a gina bandakuna miliyan 3.9 a duk shekara domin cimma burinta na 2025 na kawo karshen bahaya a fili.
Shugabar hukumar kula da ruwa da tsaftar mahalli a UNICEF, Dr. Jane Bevan ta bayyana hakan a ranar Litinin a Abuja.
Ta ce gine-ginen da ake yi yanzu a kasarnan ya kai tsakanin bandakuna dubu 180 zuwa dubu 200 a duk shekara, inda ta bayyana hakan amatsayin wanda bai wadatar ba.
A nata bangaren, Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta Tarayya, Dokta Didi Walson-Jack, ta bayyana kwarin gwiwar cewa masu ruwa da tsaki za su kara kaimi ga kokarin gwamnati na ganin an cimma manufar kawo karshen bahaya a fili a Najeriya.