On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Najeriya Na Asarar Gangar 'Danyen Man Fetur 400,000 A Kowacce Rana Sanadiyar Barayi

Gwamnatin tarayya ta koka akan yawan adadin ɗanyen man fetur da Najeriya ke asara sanadiyar ayyukan barayi , da ke kawo koma baya wajen samar da mai.

Karamin minista na albarkatun man fetur na ƙasa Timipre Sylva, shine ya bayyana hakan  lokacin da ya ziyarci gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma a fadar gwamnatin Jihar da ke Owerri.

Mista Sylva ya kara da cewa ɓata garin da ke aikata wannan laifi sun jawo adadin man da ake samarwa a rana ya ragu da wajen ganga 400,000, saboda haka a rana a maimakon a fitar da ganga miliyan 1.8 ya koma 1.4.

Sylva, ya samu rakiyar manyan kusoshin gwamnati da suka hada da ƙaramin ministan ilimi Goodluck Opiah, da babban hafsan   tsaro Janar Lucky Irabo, da shugaban kamfanin man fetur na ƙasa  NNPC Mele Kyari.

Ya bayyana zuwan nasu a matsayin babban yunkuri domin samar da dawamammar hanyar daƙile satar mai a Najeriya.

Ya kuma ƙara da cewa sun je jihar ne domin neman goyon bayan gwamnatin jihar wajen taƙalar matsalar.