Najeriya da Angola sun ki amincewa da matakin da kungiyar kasashe masu arzikin fitar da man fetur ta duniya Opec ta bukaci su dauka, na rage yawan man da suke hakowa.
Rahotonni sun bayyana cewa, kawancen Kasashen da Saudiyya ke jagoranta ba su samu cimma matsaya ba da Angola da Najeriya, wadanda suka nuna rashin amincewarsu da rage yawan man da suke hakowa.
Wani wakili a yayin ganawar ya ce ba lallai ba ne a iya cimma matsaya a tsakanin bangarorin biyu kafin taron da kungiyar ta OPEC da za’a yi a gobe 30 ga Nuwambar 2023.