Najeriya ce ke kan gaba a jerin kasashen da suka fi fama da matsalar rashin aikin yi, kamar yadda wata kididdiga ta duniya da aka fitar ta baiyana.
Najeriya ce ke kan gaba da kashi 33 da digo 3 cikin 100 a bangaren masu zaman kashe wando sai kuma kasar Afirka ta Kudu dake da kashi 32 da digo 9 cikin 100 yayin da Iran ked a kashi 15 da digo 55 cikin 100.
Rahoton ya ce mafi karancin marasa aikin yi sune suke a kasashe kamar Qatar da Cambodia sai kuma, jamhuriyar Nijar
A cewar Hukumar Kididdiga ta Kasa, yawan marasa aikin yi a Najeriya ya karu zuwa kashi 33 da digo 30 a rubu'i na hudu na shekarar 2020