Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta yi watsi da wasu rahotanni dake cewa an haramta cin taliyar Indomie, tare da tabbatar wa alumma cewa taliyar tana da inganci kuma bata da matsala.
Idan za’a iya tunawa dai jami’an lafiya a kasashen Malaysia da Taiwan sun yi ikirarin cewa an samu sinadarin Ethylene Oxide a cikin taliyar, wanda kuma sinadarin yana saka cutar daji, inda kuma aka gudanar da bincike akan taliyar da masu samar da ita.
Maikatar lafiya ta kasar Malaysia tace zata yi gaggawar bayar da umarnin yin gwaji akan dukannin nau;ikan taliyar indomie da ake yin amfani dasu a dukannin iyakokin shiga kasar.
Duk da hakan dai, Shugabar Hukumar Kula da ingancin Abinci da magunguna ta kasa, Prof Mojisola Adeyeye ta bayyana cewa NAFDAC bata haramta cin taliyar Indomie ba. Ta kuma jaddada cewa taliyar ta kasance cikin jerin kayayyakin da kasar nan ta hana shigo da su don karfafa samar da kayayyaki na cikin gida.