Hukumar kula da ingancin Abinci da Magunguna ta kasa NAFDAC ta baiyana fargabar ta kan lalacewar mafi akasarin wurin magani da ake dasu a jihar Kano.
Babban jami’in hukumar reshen jihar Kano, Kasim Idrisa ne ya baiyana haka lokacin da yake karin haske kan aiyukan hukumar a zangon farko na shekarar bana.
Ya kara da cewar hukumar zata tursasawa daukacin masu harkar magani a jihar kano komawa sabuwar kasuwar saida magani ta zamani wadda aka saka mata dukkanin kayan zamani da ake bukata dake kan titin zuwa Zariya , domin samun saukin bankado jabun maguguna da ake hada-hadarsu.
A cewarsa sama da kanfanoni 35 a nan jihar kano aka daukin matakin ladabtawa akansu a wannan zangon sakamakon aikata lefuka, wanda ya shafi yin amfani da wurin ajiyar magani maras inganci da kuma rashin bin ka’idojin hukumar ta NAFDAC.