
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC Ta ja kunnen jama’a game da yin amfani da wani maganin karin kuzari mai suna Prime Zen Black dake yawo a kasuwanni.
Hukumar ta yi jan hankalin ne ta cikin wata sanarwa mai dauke dasa hannun shugabar hukumar Mojisola Adeyeye wadda aka rabawa manema labarai a Abuja.
Ta ce ana yin maganin ne a kasar Amurika kuma akwai sinadarai masu cutarwa a cikinsa.