Daraktan yakin neman zaben Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa na goma, Sanata Opeyemi Bamidele ya ce sanatocin da ke muradin ganin Godswill Akpabio ya samu nasara, sun hallara zauren majalisar dattawa tun da karfe 4 na Asubahin jiya, domin dakile irin abunda ya faru a zaben shugaban majalisar dattawa na shekarar 2015.
Idan ba’a manta ba a shekarar 2015, Sanatocin dake goyon bayan tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, Suka yi zaman dirshan a zauren majalisar dattawan domin tabbatar da nasarar tsohon gwamnan jihar Kwara a matsayin shugabansu, A yayin da ragowar sanatocin ke ganawa da shugaban kasa Buhari a daidai lokacin da aka rantsar da sabon shugabancin majalisar.
Da yake jawabi a yayin wata liyafa da aka shirya masa domin murnar komawarsa zauren majalisar dattawa a karo na biyu, Sanata Bamidele dake wakiltar Ekiti ta tsakiya, Ya ce ya dauki tsawon kwanaki biyu batare da ya rintsa ba, domin tabbatar da nasarar Sanata Godswill Akpabio.