On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Mutun 53 Sun Kamu da Kwalara A Katsina,Yayinda Wasu Mutum 4 Suka Kamu Da Kyandar Biri

Gwamnatin Jihar Katsina ta tabbatar da mutum hudu da suka kamu da cutar kyandar biri, inda wasu 53 kuma suka kamu da cutar kwalara.

Kwamishinan lafiya na Jihar, Yakubu Danja, shi ya tabbatar da hakan a wani taro da aka shiryawa ma'aikatan lafiya.

Danja ya ce an gano sabbin mutane da suka kamu da cutar ne bayan gwaji da aka yi wa mutum 27 a baya-bayan nan.

A cewarsa, mutum tara cikin 27 din da ake zargi sun kamu da cutar sun fito daga wasu kananan hukumomi da ba a bayyana ba a jihar.

Kwamishinan ya bukaci mazauna jihar da suka bin dokokin lafiya sannan kar suyi kasa a gwuiwa wajen ziyartar cibiyar lafiya da ke kusa ko asibitoci idan suka fara ganin alamu da basu saba gani ba.

Ya ce babu dai wanda ya mutu cikin sabbin wadanda suka kamu da cutar inda tuni aka yi wa wadanda suka kamu jinya tare da sallamarsu.