On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Mutum 50 Sun Mutu Yayinda Dubbai Suka Rasa Muhallansu Sanadiyar Ambaliyar Ruwa A Jihar Jigawa

Akalla mutane 50 ne suka gamu da ajalinsu, inda da yawa suka rasa muhallan su sakamakon ambaliyar ruwa a wasu sassa daban-daban na jihar Jigawa.

Da yake jawabi ga manema labarai a birnin Dutse a ranar Asabar, babban sakataren hukumar bada agajin gaggawa ta jihar SEMA, Sani Yusuf, yace ambaliyar ta lalata dubban gidaje a jihar.

A cewar hukumomi hasashe ya nuna za a ci gaba da samun mamakon ruwan sama a 'yan kwanakin nan, sannan kuma za a sako Ζ™arin ruwa a kogin da ya hada Hadejiya da Jama'are.

Wasu da al’amarin ya ritsa da su, sun yi kaura daga kauyen Balangu, inda suka ce kusan gidaje 237 ne suka lalace, kana kuma mutane 4 ne suka mutu.

Mutanen kauyen da sauran wasu garuruwa sun tare a makarantun Firamare da sauran gine-ginen gwamnati domin neman mafaka.

''Wannan ruwan da aka shafe kwana uku ana yi duka kananan hukumomi 27 babu inda ba a samu wannan ruwan saman ba. Kuma gaskiya wannan rusau din ko'ina an same shi", in ji Yusuf Sani.

Ya kara da cewa, ''mutanen da ke zaune kan hanyar ruwa da kuma kusa da kogi mun fada musu su tashi daga wurin.''

Shugaban hukumar ya kuma ce sun samar da sansanoni na wucin gadi, da yanzu haka ke dauke da sama da mutum 1,000 da suka rasa gidajensu sanadiyyar ambaliya.

Yusuf yace gwamnatin jihar ta samar da sansanonin wucin gadi guda 11 domin kula da wadanda ambaliyar ta shafa.

A bangaren gwamnatin tarayya na yunkurin kawo musu dauki, ministar harkokin jin kai Sadiya Umar, ta ziyarci jihar dake Arewa maso yammacin kasar nan, inda ta raba musu kayayyakin tallafi.