Akalla mutane biyar ne aka tabbatar sun mutu sakamakon hatsarin jirgin kwale-kwale a kauyen Martaba da ke karamar hukumar Gwaram a jihar Jigawa.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Jigawa CP Sale Tafida shine ya tabbatar da faruwar al'amarin ta cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar DSP Lawan Shiisu Adam ya fitar ga manema labarai a Dutse.
A cewar sanarwar, a ranar Juma’a, 2 ga Satumba, 2022, wani kwale-kwalen ya kife da fasinjoji tara (9).
Al'amarin ya faru ne a kauyen Martaba karamar hukumar Gwaram ta jihar Jigawa, yayin da fasinjojin ke komawa gida bayan kammala sallar Juma’a.
Bayan samun rahoton, an tura da tawagar ‘yan sanda zuwa wurin.
An kubutar da hudu (4) a raye daga cikin fasinjojin da suka hadar da Barkeji mai shekara 60, da wasu mutum uku (3) duk a kauyen Martaba.
Yace bisa taimakon masu ruwa da tsaki anyi nasarar tsamo gawarwaki biyar (5) da suka hadar da Lukateru dan shekara 60 da Musa mai shekara 50 da Sale mai shekara 50 da Alhaji Shuaibu dan shekara 60 da Dogo mai shekara 50 dukkanninsu 'yan sansanin makiyaya na Darazau da ke jihar Bauchi.
An mika gawawwakin ga ’yan uwansu daga nan Kwamishinan ya jajantawa ‘yan uwan.
Ya kuma yi addu'a ga wadanda suka rasu.