Adadin mutanen da suka mutu a harin da aka kai na ranar Talata a karamar hukumar Mangu ta Jihar Filato ya karu zuwa 85, yayin da ake ci gaba da neman wadanda suka bace a yankunan da lamarin ya shafa.
Shugaban kungiyar ci gaban yankin, Joseph Gwankat ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba, Jim kadan bayan kammala wani taron tsaro da aka gudanar a fadar sarkin garin Mangu.
Gwankat ya baiyana cewar wandanda ake zargin sun kai harin makiyaya ne, lamarin da ya yi sanadin kashe-kashen da aka samu da kona gidaje tare kuma kuma lalata gonaki a yankunan nasu.
Daruruwan Mata ne suka zagaye fadar sarkin a lokacin da ake gudanar da taron, a wani mataki na nuna bacin ransu kan yawan hare-haren da ake kai masu.