Mutanen dake zaune a garuruwan dake kan hanyar Kano zuwa Gwarzo zuwa Dayi ,sunyi kira ga gwamnatin taraiyya data binciki yan kwangilar da ke aikin tagwaita hanyar, wadda aka yi watsi da aikin a halin yanzu.
Idan ba’a manta ba gwamnatin taraiyya ta kaddamar da aikin tagwaita hanyar mai tsawon kilomita 82 da digo 3 a ranar 11 ga watan yunin 2021 akan kudi naira bilyan 62 da milyan 700.
Daya daga cikin jagororin mazauna garuruwan Alhaji Abdullahi Kanye, ya fadawa manema Labarai cewar kiran nasu ya zama wajibi domin gano dalilin da yasa kanfanin dake kwangilar aikin mai suna CGC Nigeria Ltd Ya watsi da rabin aikin.
Bincike ya nuna cewar an gina hanyar ne tun a zamanin gwamnatin mulkin soja da Ibrahim Badamasi Babangida, Kuma tun daga lokacin babu wani gyara da aka yi mata zuwa yanzu.