Hukumar kare afkuwar haddura ta kasa, Ta tabbatar da mutuwar wasu mutane takwas, lokacin da suke dibar wani Man fetir na wata tankar mai data fadi a matsayin ganima, a kusa da babbar hanyar ore zuwa Benin a jihar Ondo.
A baya an ruwaito cewar Mutane da dama ne suka mutu cikinsu hadda wata mata mai dauke da juna biyu sakamakon ibtila’in na ranar Lahadin data gabata,To sai shugaban hukumar kare afkuwar haddura ta kasa reshen jihar, Ezekiel Son, Y a ce mutane takwas ne suka kone.
Ya ce tankar wadda babu wata lamba a jikinta ta kwacema direbanta ne sakamakon gudun wuce sa’a da yake yi, Kazalika ya ce daga bisani tankar ta kama da wuta lamarin da yayi sanadin mutuwar mutane takwas a lokacin da suke kwasar man a matsayin ganima.