Hukumar Bada agajin gaggawa ta jihar Jigawa SEMA, ta ce mutane shida ne suka mutu sakamakon mamakon ruwan sama da aka samu a karamar hukumar Kafin-Hausa dake jihar.
Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar, Yusuf Sani, ya baiyanawa manema labarai cewa mutane 65 ne suka samu raunuka a sakamakon mamakon ruwan saman da aka samu a ranar Talata.
Sani ya ce jami’an bada agajin gaggawa na gwamnatin jihar da kuma na tarayya suna tantance irin barnar da mamakon ruwan sama ya haifar, Ya kara da cewa, har yanzu ba a tantance adadin gidaje da kadarorin da aka yi asarar su ba, a sakamakon ibtila’in da aka samu.
Bugu da kari ya bukaci wadanda mamakon ruwan ya raba da muhallansu da su zauna tare da ‘yan uwansu har zuwa lokacin da za’a samar masu da matsugunni.