Kimanin mutane 30 ne suka mutu a wani kazamanin hadarin mota da ya faru akan hanyar Zaria zuwa Kano a ranar Alhamis.
Hadarin ya faru ne da misalin karfe 5 da Rabi na yammacin Ranar Alhamis a karamar hukumar Makarfi ta jihar Kaduna.
Wani shaidar gani da ido Suleiman Mohammed ya ce sakamakon wutar da ta kama motocin da abin ya shafa, da kyar mutane suka iya ceto 6 daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su.
Mataimakin kwamandan hukumar kare afkuwar hadurra ta kasa mai kula da shiyyar Zariya, Abdurahman Yakasai ya tabbatarwa manema labarai faruwar hatsarin.
Ya ce hadarin ya ritsa da wasu motocin bas kirar Toyota masu cin mutane 18 da kuma wata mota kirar Volkswagen Gulf.
Ya kuma ce a yanzu haka ana kan binciken gano bayanan wadanda hadarin ya ritsa dasu, bayan wutar data kama motocin ta kone su baki dayansu.