A yanzu haka yawan mutanen da suka rasu a sakamakon ibtila’in girgizar kasa data faru a kasashen Turkiya da Syria ya karu zuwa dubu biyu da dari ukku a cikin kwana daya da faruwar al’amarin.
Girgizar kasar mai karfin gaske ta afkawa kasashen ne da asubahin jiya , a yayin da har yanzu jami’an bada agaji ke cigaba da zakulo gawarwarkin mutanen da suka mutu.
Masu aikin ceto sun yi amfani da manyan kayan aiki da hannayensu wajen zakulo baraguzan gine-gine domin neman wadanda suka tsira, wanda a wani lokacin ake jiyo sautin neman temako a karkashin baraguzan gine-gine.