![](https://mmo.aiircdn.com/370/63ae9444eb2fc.jpg)
Akalla mutane sama da goma ne suka mutu a sakamakon tashin wata gobara a wani gidan Caca dake jikin wani otal dake kasar Cambodia akan iyakar kasar da Thailand.
Jami’an yansanda sun baiyana cewa daruruwan mutane ne ke a cikin ginin lokacin da gobarar ta tashi a gidan Cacar wanda ke a garin Poipet a ranar Larabar data gabata.
Wasu faya-fayan bidiyo da suka karade shafukan sada zumunta sun nuna yadda mutane suka rika dirowa daga saman bene, A yayin da kafofin yada labaran yankin suka ce da yuyuwar a samu karuwar mutanen da suka mutu.