Mutane hudu ne ake fargabar sun mutu a sakamakon wata arangama da aka yi tsakanin jami’an tsaro dake raka tawagar gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i da wasu ‘yan kungiyar Shi’a a yankin Bakin Ruwa dake jihar Kaduna a jiya.
Ayarin gwamnan sunyi taho mugama da mabiya mazhabar ta shi’a ne a lokacin da suke gudanar da tattakin da suka saba yi duk mako a kusa da kan babbar hanyar Nnamdi Azikiwe da karfe 4 da mintina 15 na yammaci, a lokacin da gwamnan yakai wata ziyara yankin.
Daya daga cikin ‘yan uwan wadanda suka rasa ransu mai suna Yusha’u Muhammed, Dan uwan nasa da ya gamu da ajalinsa ba, Direban motar haya ne ba ‘Dan Shi’a ba ne, Sai dai ya rasa ransa ne a sakamakon wani harsashin bindiga da ya same shi.
Wani wakilin kungiyar ta shi’a a jihar Kaduna, Abdullahi Usman ya fadawa jaridar Daily Trust cewar, dukkanin wadanda suka rasa ransu ba ‘yan shi’a ba ne, Inda ya baiyana cewar direbobin motar haya ne da suka tsaya a wata tashar mota dake kusa da wajen da abun ya faru.
Kakakin rundunar yansandan jihar DSP Mohammed Jalige ya ce a yanzu haka ana kan gudanar da bincike,kuma rundunar zata yi cikakken jawabi a nan gaba kadan.