Gwamnatin jihar Kaduna ta ce mutane 214 ne aka kashe a tsakanin watan Janairu zuwa Maris na wannan shekara a hare-haren ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda da rikicin kabilanci, hare-haren tarzoma da kuma daukar fansa a jihar.
Har ila yau, gwamnatin ta Kaduna ta ce an yi garkuwa da wasu mutane 746 a cikin tsukin wannan lokaci, kamar yadda rahoton tsaro na shekara ta 2023 da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ya gabatar jiya a Kaduna ya nuna.
Rahoton ya ce an kuma kashe ‘yan bindiga 89 a yayin da sukayi arangama da jami’an tsaro.
Ya kara da cewa ‘yan bindiga 5 sun mutu sakamakon arangamar da suka yi a tsakaninsu, wanda ya kawo adadin mutuwar ‘yan bindigar zuwa 94.
Saboda haka jimillar mutanen da suka mutu a tsawon wannan lokaci da suka hada da mazauna jihar da ‘yan ta’dda sun kai 308.