Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutane biyu a wani hadarin kwale-kwale da ya faru a karamar hukumar Ringim.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Lawan Shiisu, shine ya tabbatar da faruwar lamarin ta cikin wata sanarwa daya fitar a Dutse babban birnin jihar. Shiisu ya ce kwale-kwalen mai dauke da fasinjoji 13 suna kan hanyarsu ta zuwa ziyarar jaje, lokacin daya kife bayan da bugi wani abu.
Ya bayyana cewa biyu daga cikin fasinjoji bakwai dake cikin jirgin da suka rigamu gidan gaskiya sun hada da , Bara’atu Garba da Mahmud Surajo .
A cewarsa, an mika gawarwakin mutane ga iyalansu domin yi masu sutura yayin da sauran mutane biyar ke samun kulawa a asibiti. Ya kara da cewa har yanzu ba a ga ragowar sauran mutane shida da suka nutse a cikin ruwan ba.