Kimanin mutane 9 ne suka gamu da ajalinsu bayan wata motar matafiya ta fada dam din Fada dake karamar hukumar Gwarzo a Jihar Kano.
Ta cikin Wata sanarwa da aka fitar, hukumar kashe gobara ta jihar Kano tace ta samu kiran gaggawa ta hannun Ali Mai Faci, da karfe 06:45 na yammacin ranar asabar inda ya bayar da rahoton faruwar wani Iftila'i a dam din Fada dake Dayi a karamar hukumar Gwarzo.
Mai magana da yawun hukumar Saminu Yusif Abdullahi, yace lokacin da jami'an hukumar suka Isa wurin daga offishin kashe gobara na Gwarzo sun gano cewa wata motar Golf da ta taso daga Kano ta nufi Katsina, ta fada cikin dam din Fada.
Saminu, yace al'amarin ya ritsa da mutane 12 da suka hada da jarirai mata 2 ‘yan kimanin wata 6, sai Manyan mata 4 ‘yan kimanin shekaru 30 da 28 da 27 da 25, da kuma maza 6 ‘yan kimanin shekaru 48 da 45 da 42 da 40 da 35 da 28.
Bisa namijin kokarin jami'an kwana-kwaba da masunta na yankin an samu nasarar ceto mutane uku da ransu, yayin da mutane tara suka fita daga hayyqcinsu kuma aka kai su zuwa babban asibitin Gwarzo domin kula da lafiya, inda likitoci suka tabbatar da mutuwar mutane 9 daga cikin wadanda abin ya shafa.
A cewar wani shaidar gani da ido, ana hasashen akwai sauran mutum 1 a cikin dam din, yayinda hukumar tace za'a ci gaba da bincike kamar yadda aka saba.
Kakin hukumar kashe ta kwana-kwana a Kano Saminu Yusif Abdullahi yace kwacewar kan motar ne musabbabin faruwar al'amarin.