Kimanin mutane 79 ne suka mutu a Najeriya sanadiyar kamuwa da amai da gudawa a tare da jimillar mutane dubu 1 da 336 da ake zargin sun kamu da cutar ta kwalara ya zuwa yanzu a shekarar 2023, a cewar bayanai safa Cibiyar Yaki da Cutuka masu yaduwa da ta kasa NCDC.
Hukumar NCDC, ta shafinta na yanar gizo, ta bayyana hakan a cikin rahotonta na baya-bayan nan game da cutar kwalara.
Hukumar ta ce jihohi 12 a fadin kananan hukumomi 43 ne suka bayar da rahoton bullar cutar, inda adadin wadanda suka mutu ya kai kashi 5.9 cikin 100.
Jihohin sun hada da Kano, Katsina, Abia, Bauchi, Bayelsa, Cross River, Ebonyi, Niger, Ondo, Osun, Sokoto, da Zamfara.