On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Mutane 30 Sun Mutu A Wurin Hakar Ma'adinai Dake Abuja

ABUJA

Mutane 30 ne suka mutu sakamakon ruftawar kasa da aka samu a wani wurin hakar ma’adinai dake yankin Kuje Abuja, A yayin da ‘yan bindiga suka sace mutane 19 a yankin Bwari dake birnin taraiyyar duk a ranar Alhamis.

An baiyana haka ne a yayin wani taro da aka yi jiya  tsakanin   ministan birnin taraiyya Abuja  Nyesom Wike, da  kuma shugabannin kananan hukumomin Abuja guda  shida, Tuni dai ministan ya umarci  shugabannin suyi  gaggawar kafa  kwamitocin karkatakwana  domin saka ido  kan  aiyukan masu hakar ma’adinan.

Shugaban karamar  hukumar Kuje,  Abdullahi Sabo, Ya koka da aiyukan masu hakar Ma’adinan ta barauniyar  hanya,  Inda  yace  lasisin hakar ma’adinai da ake baiwa  ‘yan kasar China  na haddasa  matsala  ta rashin tsaro.

Daga nan ministan ya yi alkawarin ganawa da ministan kula da Ma’adinai na kasa, Dele Alake, domin magance  aiyukan masu hakar ma’adinai ta barauniyar hanya a Abuja. Haka zalika ya yi alkawarin ganawa da shugaban hukumar tsaro ta farin kaya DSS  da  kwamishinan   yansandan Abuja  domin  tattauna  yadda  za’a  kubutar da mutanen da aka sace.