Kimanin mutane 26 ne suka mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon wata gobarar daji da ta lakume gundumomi 14 na arewacin kasar Aljeriya a ranar Laraba.
Ministan cikin gida na kasar, Kamel Beldjoud ya fadawa gidan talabijin na kasar cewa mutane 24 ne suka rasa rayukansu sakamakon gobarar da ta tashi a yankin El Tarf da ke kusa da kan iyaka da kasar Tunisia, baya ga wasu biyu da suka mutu tun farkon tashinta a yankin Setif.
Hukumar kare hakkin farar hula a yankin Setif tace wasu mata biyu, Wadanda suka hada da wata Uwa mai shekaru 58 da Yarta mai shekaru 31 sun mutu a yankin sakamakon ibtila’in Gobarar Dajin.
Kazalika a yankin Souk Ahras wanda ke iyakar kasar Aljeriya da Tunisia daga gabashin kasar, an ga mutane na ficewa daga gidajensu yayin da gobarar ta bazu kafin jirage masu saukar ungulu na kashe gobara su karasa yankin.
Tun a farkon watan Agusta da muke ciki ne, Aka samu tashin gobarar Daji har Dari da Shida a kasar ta Algeriya.