Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr Aminu Tsanyawa ya tabbatar da bullar wata cutar Mashako mai saurin kisa a sassan jihar.
Alamomin cutar da rahotanni suka bayyana cewa tayi ajalin kimanin mutane 25 a jihar Kano sun hada da ciwon makogwaro da tari da kafewar yawu da dashewar murya sai kumburin wuya da rashin daidaituwar numfashi da zazzabi ko wasu lokutan da warin baki.
Kwamishinan yace a jiya ne tawagar bayar da agajin gaggawa suka yi taro domin tantance alkaluman wadanda suka mutu, da duba bayanai da kuma matakan shawo kan al’amarin.
Dr Tsanyawa, yace an sake farfado da tawagar masu bayar da agajin gaggawa a jihar Kano domin duba yanayin yaduwar cutar.
Ya kara da cewa za’a rikakebe masu cutar a asibitin kwararru na Murtala Muhammad dake tsakiyar birni, yayin da za’a samar da wasu karin cibiyoyi domin dakile yaduwar cutar.