Gwamnatin jihar Kano ta samar da wasu cibiyoyin kula da masu cutar Mashako guda ukku a jihar nan, a yayin da wadanda suka kamu da cutar yah aura 130.
Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr Abubakar Yusuf ne ya baiyana haka a ranar Alhamis, Y ace gwamnati ta dauki matakan da suka da suka dace domin dakile bazuwar cutar.
Kazalika y ace zuwa ranar Litinin mutane sama 130 ne aka kwantar akan gadon asisbiti saboda kamuwa da cutar a yayin da take ci gaba da karuwa.
Kazalika kwamishinan lafiya na jihar kano ya koka da cewar jiha kamar kano bai kamata ace tana fama da irin wannan cuta ba, inda ya zargi tsohuwar gwamnati da rashin yin rigakafi ga jama’ar jihar nan.