
Hukumar kare afkuwar hadurra ta kasa reshen jihar Filato, Tace mutane 10 ne suka rasa rayukansu a yayin da wasu 15 suka jikkata a yayin wasu hadurra biyu wanda ya ritsa da wasu motoci bakwai akan hanyar Jos zuwa Bauchi.
Kwamandan Hukumar Alphonsus Godwin ne ya baiyana haka a ranar Alhamis a birnin Jos, Yace abun alhinin ya ritsa da wata babbar mota da kuma kananan motoci 6.
Yace Babbar motar ta kwacewa direbanta wanda bai kai munzali ba, wanda hakan yasa tayi taho mu gama da motoci, al’amarin da yayi sanadin faruwar hadurran.
Daga nan sai ya shawarci masu manyan motoci dasu rika tabbatar da lafiyar ababen hawansu, tare da bibiyar direbobin, da kuma dena Saka kananan yara tuki.