Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ta ayyana yaki da daidaikun mutane da ke saye tare da boye katin zabe na dindindin, gabanin babban zabe na shekara mai zuwa.
Ta sanar da cewa, yayin da ta samu nasarar gurfanar da wani Nasiru Idris a gaban wata kotun majistare da ke jihar Sokoto, bisa laifin mallakar katinan zabe guda 101, a yanzu haka tana tuhumar wani dan jihar Kano da ba a tantance sunan ba, wanda aka same shi da katinan zabe guda 367.
A wata sanarwa dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai da wayar da kan masu zabe na INEC Festus Okoye, hukumar ta bayyana cewa mallakar katin zabe na dindindin ba bisa ka’ida ba ya sabawa sashe na 117 da 145 na dokar zabe ta shekarar 2002.
Ita kuwa, kungiyar masu kamfanonin sadarwa ATCON ta tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa tsarin kayyakin sadarwa a kasarnan na da karfin iya isar da sakamakon zabe ta hanyar kafar Internet.
Mambobin kungiyar da suka hadar da MTN da Airtel da 9Mobile da Glo, da sauran masu gudanar da harkokin sadarwa sun yi imanin cewa kayayyakin sadarwa a Najeriya sun kara habaka ta yadda za su iya yada sakamakon zabe a 2023.
Babban jami’in gudanarwa na kungiyar, Ajibola Olude, ya kawar rashin gamsuwa da shugabancin jam’iyyar APC ta nuna kan amfani da na’urar BVAS da kuma tura sakamakon zabe ta hanyar intanet.
Olude ya ci gaba da cewa Hukumar Sadarwa ta kasa NCC ta fara aikin wayar da kan jama’a a yankunan karkara.