Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce ya na sane da halin da ‘yan Najeriya ke ciki sakamakon matakai masu tsauri da ya dauka, wadanda yin hakan ya zama wajibi domin fitar da Najeriya daga cikin matsalolin da take fuskanta.
Tinubun ya ce ko gwamnatin da ta gabace shi ta fahimci irin illar da ke tattare da tallafin da ake bayarwa a bangaren man fetur, dalilin da a cewarsa ya sanya ta ki zuba tallafin na watan Yunin 2023 da ya gabata.
Shugaban ya ce da akwai wata hanya mai sauki domin fitar da Najeriya daga cikin wannan yanayi da ya dauka, amma rashin haka ya sa shi daukar wadannan matakai masu tsauri a yanzu, amma kowa zai ci gajiyar su a nan gaba kadan.
Tinubu ya kuma ce sun ware naira biliyan 100 domin sayen motocin safa safa guda dubu 3 da za’a raba su a kananan hukumomi 774 domin bunkasa sufurin jama’a.
Haka kuma, shugaban kasaBola Ahmed Tinubu ya sanar da bayar da tallafin Naira biliyan 75 ga masana’antu, inda ya ce harkokin kasuwanci 75 za su ci gajiyar tsarin a cikin watanni tara da ke tsakanin zango na uku na shekarar 2023 zuwa watan Maris na 2024.
Shugaban ya kuma nunar da yadda gwamnati ta amince da kananan masana'antu da matsakaitan masana'antu da kuma sassan da ba na yau da kullun ba amatsayin masu kawo ci gaba.
Ya bayyana wani asusu na Naira biliyan 125 don karfafawa fannin.