Wasu Alamu na nuni da cewa gwamnatin tarayya na neman tallafin kasar Masar domin kwaso ‘yan Najeriya da yawansu ya kai dubu 5 da 500 da suka makale a Sudan ta hanyar garin Luxor na kasar ta Masar.
Daraktan ayyuka na musamman na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa NEMA, Dr Onimode Bandele, ya ce gwamnatin tarayya na ganawa da jami’an gwamnati a Masar kan yadda za a fitar da ‘yan Najeriya daga kasar Sudan.
Har ila yau, Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama, a wata zantawa da gidan talabijin na Channels a daren jiya, yace gwamnati ta kammala shirye-shiryen kwashe 'yan Najeriya da ke Sudan ta hanyar Motoci.
A cewarsa, Najeriya saboda dalilai na tsaro zata samu izini daga gwamnatin Sudan kafin a kwashe Mutanen.