Majalisar dattawa tace zata gudanar da bincike akan cefanar da filyen tashi da saukar jiragen sama na Aminu Kano da Nnamdi Azikiwe dake Abuja, tana mai cewa binciken ya zama wajibi a sakamakon hnyar da aka bi aka cefanar da filayen jiragen saman a bude ba.
Matakin da Majalisar dattawan ta dauka na yin bincike akan cefanar da fijin jiragen saman ya biyo bayan wata bukata da sanata Kawu Sumaila ya gabatar, wanda yace cefanarwar anyi ta ne ba bisa ka’ida.
Ya bayyana cewa ma’aikatar sufurin jiragen sama ta kasa ba itace mai filayen ba kuma bata da ikon kula da ko wane filin jirgin sama a kasarnan, wanda yace hukumar FAAN ce ta mallaki filayen jiragen saman kuma it ace take kula da su.
Ya kuma kara da cewa majalisar zartaswa a ranar 17 ga watan Mayu ta amince da cefanar da filin jirgin sama na Aminu Kano na tsawon shekaru 30.