Kungiyar zauren cigaban tattalin arzikin Arewa ta bayyana cewa matsakaicin asarar kudi na mako-mako sakamakon rufe iyakokin Nijar da Najeriya ya kai Naira biliyan 13.
Kungiyar ta shaidawa manema labarai a Abuja cewa, ‘yan kasuwar Arewacin Najeriya na da kwantenar kayan gwari kimnain.dubu 2 da suka makale sakamakon rufe iyakokin wanda ya biyo bayan juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Nijar.
Shugaban kungiyar, Alhaji Ibrahim Shehu Dandakata, ya ce bisa kididdigar shekarar 2022, cinikayyar yau da kullum tsakanin kasashen biyu ta kai Naira biliyan 171, yayin da ake kiyasin ciniki na yau da kullum ya kai Nwira billiyan dari 5 da 15, galibi na kayayyaki masu lalacewa.
Ya kara da cewa al'ummar Nijar kusan miliyan 25 ne kuma kusan kashi 70 mazauna garuruwan da ke kusa da Najeriya ne.