On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Mun Samu Tabbacin Shugaban Kasa, Kan Fara Aikin Matatar Mai Ta Fatakwal Zuwa Watan Disamba - NLC

Kungiyoyin kwadago a kasarnan na  NLC da TUC sun dakatar da zanga-zangar da suka fara a jiya bayan sun gana da shugaban kasa Bola Tinubu.

Sun bayyana cewa za a baiwa gwamnatin tarayya lokaci domin ta cika alkawuran da ta dauka.

A karshen ganawar ta yammacin jiya laraba, shugaban kungiyar ta NLC, Joe Ajaero, ya shaida wa manema labarai cewa, kungiyoyin za su baiwa gwamnati wani lokaci, yana mai bayyana ganawar da shugaban kasar a matsayin daya daga cikin nasarorin da aka samu a zanga-zangar.

Ajaero ya ce Tinubu ya ba su tabbacin cewa matatar mai ta Fatakwal za ta fara aiki a watan Disamba kuma za a cimma matsaya kan mafi karancin albashin ma’aikata.

Ya kara da cewa shugaban ya kuma yi alkawarin kaddamar da taswirar da za a iya amfani da ita wajen fadada aiki da  makamashin iskar gas a mako mai zuwa kuma bisa ga wannan tabbacin, kungiyoyin sun yanke shawarar rungumar sabuwar hanyar tattaunawa.