On Air Now

Maraicen Asabar

6:00pm - Midnight

Mun Gano Manyan Matsalolin Makabartu - Gwamnatin Jihar Kano

Gwamnatin jihar Kano ta ce zata dauki matakan magance manyan matsalolin da makabartu ke fuskantar a cikin kwaryar birnin jihar.

Shugaban kwamitin kuma kwamishinan ma'aikatar raya karkara da cigaba al'umma Alhaji Hamza Safiyanu Kachako shi ne ya bayyana haka ne jim kadan bayan samun rahoto daga shugabannin da suka zagaya makabartun domin tantance matsalolin.

Ya ce zagayen ya gano rashin ingantacciyar Katanga da  magudanar ruwa da fitulun tsaro da rijiyoyin burtsatse, masu gadi da dai sauransu amatsayin manyan matsaloli ga makabartu.

Hamza Safiyanu Kachako ya kara da cewa ma'aikatar za ta mika rahoton ga gwamna Abba Kabir domin amincewar sa.

Daga nan sai ya bada tabbacin gwamnatin jihar Kano ta himmatu wajen inganta yanayin makabartu.

Kwamishinan ya gargadi mutane da su guji zubar da shara a makabartu.

Daga cikin wuraren da aka ziyarta akwai makabartar Gama  da Unguwa Uku DA Tarauni da kuma Court Road.

Sauran sun hada da makabartar Gandun Albasa da ‘Dan Agundi da Hauren Shanu dake karamar hukumar Gwale.