Rundunar ‘yan sanda a jihar Bauchi ta fara gudanar da bincike akan zargin yiwa wata jaririya ‘yar wata 18 fyade da hallaka wata yarinya ‘yar shekara 13 a Jihar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar SP Ahmad Wakil ya fitar jiya asabar a bauchi, yace an kama wani mutum dan shekara 59 bisa zargin aikata fyaden.
Ya kara da cewa an kuma kama mutum 2 bisa zargin hada baki wajen kisan yarinyar.
Wakil yace Nenkat Danladi, yace mahaifiyar jaririyar ta kai rahoton faruwar al’amrin ga offishin ‘yan sanda na Yelwa tun ranar 8 ga watan Agusta da muke ciki.