On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Muktar Yarima Zai Daukaka Kara Kan Hukuncin Kwace Kujerar Wakilcin Tarauni A Majalissar Tarayya

‘Dan majalisar wakilai da kotu ta soke nasararsa ta zaben 2023, Mukthar Umar-Zakari na jam’iyyar NNPP daga jihar Kano zai garzaya kotun daukaka kara domin kalubalantar hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke bisa zargin takardar shaidar jabu.

Umar Zakari, daga  mazabar Tarauni a majalisar tarayya, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Abuja.

Kwamitin mutum uku na kotun, karkashin jagorancin mai shari'a I.P. Chima, ya yanke hukuncin cewa bai cancanci tsayawa takara ba bayan ya yi jabun takardun shaidar firamare.

Sai dai Umar-Zakari ya musanta gabatar da takardun jabun ga INEC domin zaben na 2023, yana mai cewa an samu sabani a cikin takardun sa saboda sauya suna, wanda aka yi bisa doka.