Mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan aiyuka na musamman da al’amuran da suka shafi cikin gida, Toyin Subaru ya baiwa yan Najeriya tabbacin cewar bullo da motocin Bass masu amfani da gas zai temaka wajen rage farashin gas zuwa naira 230 akan kowanne kilo giram daya.
Hakan na zuwa ne a yayin da gwamnatin tarayya ke shirin baza motocin bas masu amfani da gas har guda dubu 11 da 500 zuwa sassan kasar nan daga makon gobe , a wani mataki na saukaka yanayin gudanr da zirga-zirga.
Ya ce matakin zai temaka wajen saukakawa yan Najeriya kimanin kaso 2 cikin 3 a bangaren gudanar da sufuri da kuma karkafa yin amfani da makamashin gas a maimakon man fetir.
Hadimin shugaban kasar ya baiyana haka a ne a yayin wnai taron masu ruwa da tsaki da aka shirya a bankin masana’antu dake Abuja.