On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Ministocin Buhari Sun Fara Mika Ragamar Aiki Gabanin Karewar Wa'adin Mulki

Kwanaki biyar gabanin karewar wa'adin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ministoci sun fara mika ragamar aiki ga  manyan sakatarori a ma'aikatunsu gabanin rushe majalisar zartaswa.

A ranar litinin 29 ga watan Mayu na 2023 wa'adin mulkin shugaba Buhari na shekaru 8, wanda ya fara daga ranar 29 ga watan Mayun 2015 zai kare.

Wata majiya ta fadawa manema labarai cewa a yau ne Ministoci zasu ajiye aiki hukumance duk da cewa Shugaba Buhari bai bayyana rusa majalisar ministocin tarayya ba.

Bayanai sunce ministan tsaro, Bashir Magashi, ya umurci babban sakataren ma’aikatar Ibrahim Kana da ya karbi ragamar aiki.

Shima ministan wasanni, Sunday Dare, zai  mika ragama ga  babban sakatare na ma’aikatarsa Alhaji Ismaila Abubakar ayau.

………….