Yayin da ake tsaka da fuskantar kalubalen tsaro a wasu sassan kasar nan , Ministan Tsaro, Abubakar Badaru, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da yi wa gwamnati mai ci addu’a, musamman masu rike da mukaman kula da tsaron kasa.
Badaru, wanda ya yi wannan roko ne a ofishinsa da ke Abuja a lokacin da ya karbi bakuncin wata tawaga ta musamman daga Ja gawa karkashin jagorancin gwamnan jahar, Malam Umar Namadi, ya ce irin sarkakiyar kalubalen tsaro da ake fuskanta a Najeriya, Babu abunda mutum yake bukata sai addu’o’in samun nasara.
A cewarsa, duk da cewa aikin da ke gabansu na da yawa, amma sun kuduri aniyar shawo kan kalubalen da ake fuskanta, inda ya bukaci ‘yan Najeriya da su mara musu baya ta kowane fanni da suka hada da yi masu addu’o’i domin ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasa.
Shima a nasa jawabin gwamnan jahar Jigawa, Umar Namadi, wanda ya jagoranci sarakunan gargajiya da malaman addini da ‘yan kasuwa da masu rike da mukaman gwamnati da suka fito daga ja har a yayin ziyarar , ya ce sun je wajen ministan tsaron ne domin taya shi murna tare da ba shi tabbacin samun goyon bayansu a kowane lokaci.