On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Ministan Harkokin Waje Zai Wakilcin Najeriya Wajen Rabbata Hannu Akan Shirin Aikin Hajjin 2023

Babban jami’in gudanarwa kuma shugaban hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, ya mika goron gayyata ga ministan harkokin wajen kasarnan Ambasada Yusuf Tuggar domin ya wakilci Najeriya a wajen rattaba hannu kan yarjejeniyar aikin hajjin 2024 da ake sa ran za a fara a farkon watan Janairun 2024.

Ya sanar da hakan ne lokacin da ya gana da Ministan domin neman goyon bayan ma’aikatar a harkokin Hajji da  Umrah da sauran harkokin ofishin jakadancin. 
Bayanin hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mataimakiyar daraktar hulda da jama’a ta NAHCON, Fatima Sanda Usara,  ta  fitar a ranar Alhamis. 
Alhaji Kunle Hassan ya gabatar da hukumar ta NAHCON ga Ministan inda ya bayyana ma’aikatar harkokin wajen kasarnan a matsayin mai ruwa da tsaki a harkar aikin Hajji. 
Alhaji Hassan ya kuma Shugaban ya bayyana cewa an mika goron gayyatar da wuri domin bai wa Ministan isasshen lokaci. 
Da yake mayar da jawabi, Ambasada Tuggar ya tabbatarwa Shugaban Hukumar NAHCON cewa a shirye ma’aikatar take wajen samar hadin kai da nufin saukaka al’amuran mahajjata da kuma daukaka martabar kasar nan. 
Ya kuma bayyana aniyarsa ta shiga rattaba hannu kan yarjejeniyar aikin hajjin a watan Janairu. 
ukkan shugabannin biyu sun amince da yin aiki tare wajen inganta ayyukan aikin hajji.